Amnesty International ta bayyana matuƙar damuwa kan abin da ta kira ƙaruwar take haƙƙin faɗin albarkacin baki a Jihar Kano, inda ta ce ana kama da tsare mutanen da ke sukar Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na Facebook a safiyar yau, ta ce tana cikin damuwa kan yadda ake kama, tsarewa da kuma gallaza wa mutanen da kawai suka yi suka ko suka bayyana ra’ayinsu game da gwamnan.
Ƙungiyar ta zargi cewa a mafi yawan lokuta, ana kama waɗannan mutane ne ko kuma a ba su abin da ake kira “gayyata” daga Department of State Services (DSS).
“Wannan yanayi na ƙaruwa kuma yana take haƙƙi da haifar da matsalar tsoro a tsakanin al’umma, tare da jefa haƙƙin faɗin albarkacin baki cikin haɗari,” in ji Amnesty International.
Mutanen da Aka Ambata
A cewar ƙungiyar, Abba Ibrahim Hussain, ɗalibin shari’a a Jami’ar Northwest da ke Kano, an kama shi ne a gidansa da safiyar Lahadi ta hannun jami’an DSS masu ɗauke da makamai, bisa zargin sukar gwamnan.
Har yanzu yana tsare, kuma akwai yiwuwar ya rasa jarabawarsa da ake yi a jami’ar.
Haka kuma, an ce Aminu Warkal, wanda aka bayyana a matsayin mai tasiri a kafafen sada zumunta kuma mai sukar gwamnati, an tsare shi na tsawon sa’o’i biyar bisa zargin “cin zarafin gwamna.”
Ƙungiyar ta kuma ce Samir Hanga, Dan sanata Kano ta tsakiyar, Rufai Sani Hanga, ya fuskanci abin da ta kira “barazana” daga DSS saboda sukar gwamnan, kafin daga bisani a sake shi bayan yi masa tambayoyi.
A wani lamari, an ce Abdulmajid Danbilki Kwamanda an kama shi makonni biyu da suka gabata, kuma an tilasta masa janye wasu kalamai na sukar da ya yi wa Gwamna Abba Yusuf.
Haka zalika, Amnesty ta yi zargin cewa an kama tare da tsare wani matsashi Saifullahi Abubakar saboda yin wani bidiyon barkwanci a TikTok da ya shafi gwamnan.
“Yin barkwanci ko suka ga masu mulki ba laifi ba ne. Babu wanda ya fi ƙarfin a yi masa suka,” in ji ƙungiyar.
Kira ga Mahukunta
Amnesty International ta buƙaci hukumomin Najeriya da su mutun ta, kuma su kare tare da tabbatar da haƙƙin kowa na faɗin albarkacin baki, tana mai cewa kama masu suka ba abu ba ne da ya dace a cikin al’umma mai bin tafarkin dimokuraɗiyya ba.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wata sanarwa daga Gwamnatin Jihar Kano ko DSS dangane da zarge-zargen da ƙungiyar ta yi.
