Hukumar Kula bada agajin gaggawa ta kasa NEMA tare da Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya sun fara tattaunawa kan yadda za a tallafa wa al’ummar da ambaliya ta shafa a ƙaramar hukumar Mokwa ta Jihar Neja, da kuma yadda za a inganta shirin kare kai daga bala’o’i a gaba.
Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya Trond Jensen7,yayin ganawa da Darakta Janar ta NEMA Hajiya Zubaida Umar a babban ofishin hukumar da ke Abuja,y ace Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan irin halin da mutanen yankin Mokwa ke ciki sakamakon mummunar ambaliya da ta afku a baya-bayan nan.
A cewar wakilan duka bangarorin, akwai bukatun gaggawa da suka hada da abinci, matsuguni, kula da lafiya da tsaftar muhalli ga al’ummar da lamarin ya shafa.
Zubaida Umar ta jaddada cewa hukumar NEMA na ci gaba da bibiyar halin da ake ciki tare da haɗin gwiwa da hukumomin jihohi da ƙungiyoyin agaji domin samar da mafita ta gaggawa da na dogon lokaci.
Daga bisani ta bukaci haɗin kai daga kowane mataki domin kare lafiyar jama’a da tabbatar da cewa an ɗauki darasi daga abin da ya faru.
