Adadin waɗanda suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwan da ta afka wa Indonesia makon da ya gabata yanzu ya haura mutum 500.
Masu ceto na ci gaba da ƙoƙarin isa yankunan da abin ya shafa.
An rawaito cewa ambaliyar ruwan ta faru ne sakamakon guguwa mai dauke da ruwan sama da ba kasafai ta taso daga daga Tekun Malacca.
Ambaliyar ta shafi jihohi uku kuma ta shafi rayuwar kusan mutum milyan 1.4, a cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar.
Har yanzu ba a san inda mutum 500 suke ba, yayin da dubban mutane ne suka samu raunuka.
Indonesia dai na daga cikin ƙasashen Asiya da suka fuskanci ruwan sama mai tsanani a kwanakin baya.
Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar rufe Masallacin Juma’a a Katsina.
Barazanar Bam Ya Tilasta Saukar Jirgin Mahajjata a Indonesiya
Ma’aikatan agaji na ƙoƙarin kai ɗauki ta hanyar tafiya a ƙafa ko kan babur, domin hanyoyin da yawa ba su iya ɗaukar manyan motocin ceto.
Hotunan da suka fito daga yankunan sun nuna gadoji da ambaliya ta wanke da hanyoyi cike da laka da tarkace, da kuma manyan katakai da suka taru wuri guda.
