Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, William Troost-Ekong, ya sanar da yin ritaya daga taka wa ƙasar leda.
Ekong mai shekara 32 ya sanar da hakan ne a sanarwa da ya sa shafukansa na sada zumunta.
Bayan da mai horarwa Eric Chelle ya zaɓe shi cikin tawagar farko ta ‘yanwasan da za su wakilci Najeriya a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2025.
Ɗanwasan bayan ya buga wa Super Eagles wasa 83 tare da cin ƙwallo takwas cikin shekara 10, shi ne ɗanwasa mafi hazaƙa a gasar Afcon ta 2023 da aka yi a Ivory Coast, inda Najeriya ta ƙare a mataki na biyu.
A watan Agustan 2024 ne Ekong ya koma taka wa ƙungiyar Al-Kholood ta Saudiyya leda daga PAOK ta ƙasar Girka.
