
Mazauna karamar hukumar Dala sun bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC da ta binciki dan majalisar su na tarayya Aliyu Sani Madakin Gini kan yanda yake tasarrufi da kudaden ayyukan mazabun da gwamnati ke bashi.
Hakan na kunshe ne cikin wata takardar korafi da hadakar kungiyoyin ci gaban al’ummar yankin suka aikewa hukumar ta ICPC wadda ta samu sanya hannun Mustapha Hassan.
A cewar takardar, akwai bukatar Dan majalisar yayi bayani akan ayyukan mazabun da yake gudanarwa, wadanda basu da inganci kwata-kwata idan aka kwatanta da kudaden da ake bawa ‘yan majalisu wajen gudanar da ayyukan Mazabu.
Kungiyoyin sun bada misali da ayyukan titin Mazabar Gobirawa wanda ya wuce ta gaban gidan Marigayi Sani Mai Ishiriniya, da titin Cross Fire zuwa Kofar Ruwa, wadanda suka ce ko kusa basu da nagartar da za’a ce dan majalisar tarayya ne ya gudanar da su.