
Alhaji Aliko Dangote attajirin da ya fi kowa kudi a Africa na daga cikin manyan bakin da suka gaisa da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da shugaban ya ke yi a Qatar a ranar Laraba.
A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da aka gabatar da Dangote ga Trump, a cikin jerin fitattu kuma hamshakan mutanen da suka yi jerin gwano don gaisawa da Shugaban na Amurka wanda ke tsaye kusa da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.
Wannan gaisawar ta kasance cikin jerin tarukan diflomasiyya da kasuwanci da ke cikin rangadin Trump a yankin Gabas ta Tsakiya.
Alhaji Dangote, wanda shi ne shugaban kamfanin Dangote Group, an hangi lokacin da yake gaisawa da Trump kafin daga bisani ya wuce ya gaishe da Sarkin Qatar da kuma matarsa.
Ziyarar Trump Qatar
Shugaba Trump ya isa filin jirgin saman kasa da kasa na Hamad a kasance cikin kima da alfarma, inda jiragen yaki suka raka Air Force One zuwa birnin Doha, yayin da jerin motocin sa suka hada da sabuwar motar zamani ta Tesla Cybertruck.
Daya daga cikin manyan abubuwan da suka dauki hankalin duniya a ziyarar ita ce sanya hannu kan wata babbar yarjejeniya tsakanin kamfanin jiragen saman Qatar Airways da Boeing.
Yarjejeniyar, wadda ta kunshi sayen jirage har guda 210 masu darajar kimanin dala biliyan 96, na daga cikin mafi girma da kamfanin Boeing ya taba samu a tarihin sa.