
Dan wasan Kano Pillars, Ahmed Musa, zai jagoranci tawagar Super Eagles a gasar Unity Cup da za a gudanar daga 26 zuwa 31 ga Mayu, 2025, a birnin London, Ingila.
A wata sanarwa, mataimakin daraktan yada labarai na Kano Pillars, Ismail Abba Tangalash, ya tabbatar da cewa an gayyaci Musa zuwa tawagar Super Eagles a gasar da za ta hada kasashe hudu: Najeriya, Ghana, Jamaica, da Trinidad & Tobago.
Ismail Abba Tangalash ya ce, Kyaftin Ahmed Musa ya jagoranci nasarorin Kano Pillars a kakar bana, inda ya jefa kwallo takwas kuma ya taimaka wajen ci kwallo biyu a gasar NPFL.
Gasar Unity Cup na daya daga cikin muhimman tarukan wasanni da ke ba da damar daga sunan kasashe da kuma karrama ‘yan wasan kwallon kafa daga duniya.