
Wata kotu a Afrika ta Kudu ta yanke wa ‘yan ƙasar China bakwai hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari, bayan samunsu da laifin safarar ɗan adam da azabtar da su ta hanyar tilasta musu ayyukan bautar da suka sabawa ɗan Adam.
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da maza huɗu da mata uku, kuma an cafke su tun farkon shekarar nan, kafin fara gurfanar da su a gaban kotu.
Hukuncin ya biyo bayan shaidun da kotu ta tabbatar da cewa sun aikata laifukan da ake tuhumarsu da su.
Rahotanni daga hukumomin Afrika ta Kudu sun bayyana cewa mutanen da aka safararsu su ne ‘yan ƙasar Malawi guda 91, ciki har da ƙananan yara 37.
An ce waɗanda lamarin ya shafa sun kasance cikin mawuyacin hali na bautar zamani, inda aka killace su a wani kamfanin kasar Sin da ke cikin birnin Johannesburg, ana tilasta musu aiki ba tare da albashi mai kyau ko ‘yanci ba.
‘Yan China da ke gudanar da kasuwanci a Afrika ta Kudu na yawan ɗaukar ma’aikata daga ƙasashen ƙetare, musamman daga yankin kudancin Afrika, saboda sauƙin biyan su albashi.
Sai dai mahukunta sun bayyana damuwa kan yadda da dama daga cikinsu ke amfani da wannan damar wajen tauye haƙƙoƙin ma’aikata tare da hana su ‘yancin fita ko tuntubar danginsu.