Shugaban ƙasar Afirkata Kudu Cyril Ramaphosa ya tabbatar da karɓar Falasɗinawa 153 da Isra’ila ta tura ƙasar ba tare da tintiɓar su ba.
Ramaphosa ya shaidawa manema labarai cewar, waɗannan Falasɗinawa an sanya su ne a cikin jirgi zuwa Nairobi, kuma daga bisani a ka tasa keyar su zuwa ƙasarsa ba tare da cikakkun takardu ba.
Shugaban ya ce sun karɓe su a ƙarƙarshin matakan jinkai saboda irin yanayin da suka samu kan su da kuma inda suka fito.
Rahotanni sun ce waɗannan Falasɗinawa sun kwashe sa’oi 12 a cikin jirgi, kafin daga bisani wata ƙungiyar agaji a Afirka ta Kudu da ake kira ‘Gift of the Givers’ ta ce za ta basu wurin zama a ƙasar.
Ramaphosa ya ce babu tantama wannan wani shiri ne na Isra’ila na korar Falasɗiwan daga yankin su na Gaza.
Daga cikin Falasɗinawan 153 da suka isa ƙasar, 23 sun bar fice zuwa wasu ƙasashe, yayin da 130 yanzu haka suna Afirka ta Kudu.
Ko a ranar 28 ga watan jiya, wani jirgi ɗauke da Falasɗinawa 176 ya isa Johannesburg, wato ƙasar dake sahun gaba na goyan bayan Falasɗinawan a duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun yi tayin kwashe Falasɗinawan daga Gaza zuwa wasu ƙasashe domin mayar da yankin wani wurin yawon bude ido na duniya, matakin da Majalisar Dinkin Duniya da ƙasashen Larabawa da kuma Ƙungiyar ƙasashen Turai ke adawa da shi.
