Al’ummar Karamar Hukumar Shanono ta yi godiya tare da nuna jindadi dangane da ziyarar ta’aziyya da Sarkin Kano Muhammad Sunusi II, ya kai karamar hukumar bayan harin yan ta’adda.
Shugaban Karamar Kukumar Alhaji Abubakar Barau ya yi godiya ga sarkin a ranar Lahadi a yayin ziyarar.
“Tabbas mun ji dadin wannan ziyara sannan kuma a matakin karamar hukuma gwamanati tana baiwa jami’an tsaro dukkanin abin da suke bukata”. In ji shi.
Sarkin na Kano ya jajantawa al’ummar yankin tare da bayyana masu cewa masarautar Kano tana tare dasu a kowanne irin hali.
A yayin ziyarar sarkin ya samu tarba daga dubban al’ummar karamar hukumar da suka hada da jmai’an gwamnati da ma’aikata dama manoma da makiyaya.
