
Jam’iyyar Haɗaka ta African Democratic Congress (ADC) ta zargi Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da zama ‘ƴar koren jam’iyyar APC mai mulki, tare da zabar mutanen da take gudanar da bincike a kansu bisa la’akari da siyasa.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta bayyana cewa halin da EFCC ke ciki yanzu na buɗe shari’o’in da aka riga aka kammala, da fito da takardu na shekaru da suka gabata, har ma da matsa wa mambobin jam’iyyar ba shi ne aikin da aka san hukumar da shi a baya ba.
Jam’iyyar ta ce a kwanakin nan wasu daga cikin mambobinta sun samun sakonnin gayyata daga EFCC, waɗanda, a cewarta, suna da alaƙa da siyasa.
ADC ta kuma yi zargin cewa hukumar ta daina gudanar da bincike kan mambobin jam’iyya mai mulki, inda ta mayar da hankali kan ƴan hamayya waɗanda ba su aikata laifi ba.
Ta yi kira ga ƴan Najeriya, ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu, da su yi watsi da abin da ta kira “kama ƙarya” da EFCC ke yi domin cimma manufofin siyasa.