
Jam’iyyar (ADC) ta caccaki gwamnatin Tinubu bayan amincewar Majalisar Dokoki Na karbo wani sabon bashin dala biliyan 21 daga waje
A cewar jam’iyyar, Tinubu ya karbo bashin da ya haura tiriliyan ₦200 ba tare da wani ci gaba a zahiri ba, ko kuma farfadowar tattalin arziki da zai tabbatar da halaccin wadannan basussuka .
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya rattaba hannu, ADC ta zargi Shugaba Tinubu da zarce wanda ya gabace shi wajen cin bashin, abinda ke jefa makomar kasar cikin mawuyacin hali
Jam’iyyar ta kuma soki Majalisar kasa, tana mai cewa ta zarga da zama yan amshin shata “rubber stamp”.
“Jam’iyyar (ADC) tace ta damu sosai game da halin are aren da gwamnatin Tinubu ke yi.