Rundunar yan sandan jihar Adamawa sun sake ƙaddamar da bincike kan ƙorafin mutane uku da aka watsawa acid a shekarar 2023 data gabata.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa, an kai rahoton lamarin tun a lokacin amma ba a samu wanda ake zargi ba bayan binciken farko.
Rundunar ta ce an sake buɗe binciken domin gano mutanen da suka aikata laifin, bayan sake samun ƙorafe-ƙorafen jamaʼa da wadanda abin ya shafa.
Sanarwar ta bayyana cewa Kwamishinan ’Yan Sanda ya umurci sashen bincike da ya sake nazarin dukkan bayanan lamarin tare da tattara duk wasu hujjoji da bayanai da za su taimaka wajen gano duk wanda ke da hannu a lamarin.
