
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana talauci a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo tsaiko ga cigaban duniya.
Atiku ya bayyana haka ne a shafukansa na sada zumunta a cikin jawabinsa na Ranar Yaƙi da Talauci ta Najeriya, inda ya ce abin takaici ne yadda Najeriya ta kasance gaba-gaba cikin ƙasashen da suka fi fama da talauci.
A cewar Atiku, manyan abubuwan da suke jawo talauci sun haɗa da “jahilci da rashin tsaro da cututtuka, sannan ya yi kira ga gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen magance matsalar.
Ya ce abin ban haushi ne a ce Najeriya na cikin ƙasashen da aka fi talauci, hakan ce ta sa ya bukaci da a ba al’ummar ƙasar nan muhimmanci domin magance matsalar ta talauci.