
Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta girmama marigayi dattijon kasa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata girmamawa ta musamman.
Majalisar yi hakan ne a zamanta na ranar Talata.
‘Yan majalisar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya sunan Marigayin a wani muhimmin gini ko wurin tarihi na kasa, a matsayin karramawa da girmamawa la’akari da irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma da kuma kasa baki daya.
Mataimakin Shugaban Majalisar Sanata Barau I. Jibrin ne ya jagoranci gabatar da kudirin tare da hadin gwiwar Sanata Rufai Hanga da kuma Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila dukkaninsu daga jihar Kano.
Kudirin ya samu karbuwa daga sauran ‘yan majalisa, wanda hakan ya nuna cikakken goyon bayan majalisar kan bukatar.
Alhaji Aminu Dantata ya shahara a fannin kasuwanci da taimakon jama’a da hidima ga addini da kuma al’umma.
Majalisar ta bayyana cewa, gudummawar marigayin ya cancanci a rika tuna wa da shi ta hanyoyi na musamman domin karfafa wa matasa gwiwa da kuma koyi da irin rayuwar sadaukarwa da kishin kasa da ya yi.