
Za buga wasan ne a Filin wasa na Godswill Akpabio dake Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.
Najeriya za ta kara da Zimbabwe a yau Talata a wasan rukunin C na neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya na 2026.

Najeriya ita ce ta huɗu a rukunin da maki 6 yayin da Zimbabwe mai maki uku ita ce ta ƙarshe a rukunin.
Afirka ta Kudu kuma ita ce ta ɗaya a rukunin wadda take da maki 10.
Tuni gwamnatin jihar Akwa Ibom ta saye tikitin shiga kallon kwallon 30,000 don rabawa jama’a kyauta don kallon wasan.