Daga Hafsat Buhari
Kungiyar Dillalan man fetur ta kasa IPMAN, ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sa tallafi a danyen man da ake sayar wa matatun cikin gida.
Kakakin IPMAN, Chinedu Ukadike ne ya bayyana hakan a hirarsa da ‘yan jaridu a ranar Litinin.
“Idan aka sa tallafi a danyen mai, hakan zai taimaka wajen rage tasirin tashin farashin fetur da ka iya biyo bayan hauhawar farashin danyen mai a duniya.
“IPMAN na kuma son a faɗaɗa tsarin cinikin danyen mai da Naira, ba ga matatar Dangote kaɗai ba, har da sauran matatun da ke aiki a ƙasar”. In ji shi.
Ukadike kuma ce, farashin danyen mai yana sauyawa akai-akai a kasuwannin duniya, kuma duk wani canji kai tsaye yana shafar farashin fetur, dizal da sauran kayayyakin mai.
Sannan ya yi kira ga gwamnati da ta samar da wata yarjejeniya ta musamman kan farashin danyen mai ga matatun cikin gida, hakan zai zama kariya daga tashin farashi, tare da tabbatar da daidaito ko da farashin danyen mai ya tashi a duniya.
