Hukumar Kula da Lafiya Ta Majalisar Dinkin Duniya Duniya (WHO) ta yi kira da a faɗaɗa tare da sauƙaƙa hanyar samar da alluran rage ƙiba.
WHO ta ce, matakin babban ci gaba ne yaƙi da matsalar ƙibar da ta wuce kima a duniya. Shawarar farko da WHO ta bayar kan amfani da alluran – nau’i GLP-1, samfurin Mounjaro da Ozempic, – ta ce amfani da magungunan na tsawon lokaci tare da cin abinci mai lafiya da motsa jiki za su taimaka wajen rage ƙiba.
Hukumar ta ce, tsadar magungunan na daga cikin manyan ƙalubalen samun maganin.
Lamarin da ya sa mutane da dama ba sa iya samunsa. Fiye da mutum biliyan ɗaya ne ke fama da matsalar ƙibar da ta wuce kima a duniya.
