
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana takaicin harin da yan ta’adda ke kai wa jihar Filato, ya kuma umarci gwamnan jihar Caleb Muftwang ya gaggauta daukar matakan kawo karshen zubar da jinin da ake yi a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin
Umarnin na zuwa ne bayan da wasu iyalan wadanda harin kauyen Zikke dake karamar Hukumar Bassa ya shafa suka nuna matukar damuwa da yadda ake fama da rikici a jihar.
Kafin sanarwar, shugabancin kungiyar kiristocin jihar ta shirya gudanar da zanga zanga kan matsalar tsaro a jihar.
Ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta bayar da dukkanin abubuwan da ake bukata wajen magance matsalar.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ƙauyen Zike da ke yankin Ƙaramar Hukumar ta Bassa, suka kuma ƙona wasu ƙauyukan da dama tare da yin sace-sace da lalata duk wani abu da su ka ci karo da shi.
Mai ba wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Admiral Shipi Gakji mai ritaya, ya ce an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin.
Rahoton baya bayan nan ya bayyana cewa harin karshe da aka kai jihar ya kashe akalla mutum 50.
Allah-Wadai da lamarin
Kungiyar kare hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta bayyana kisan a matsayin sakacin hukumomin tsaro.
Ta kuma bukaci mahukunta su tashi tsaye wajen kiyaye rayukan al’umar kasar nan.
Shugaban Kungiyar a Najeriya Isah Sanusi a wata sanarwa da ya fitar, ya yi Allah-wadai da harin
Wani masanin tsaro, Kyaftin Abdullahi Bakoji Mai ritaya ya ce, hare-haren na ‘yan kwanakin nan alama ce ta karancin jami’an tsaro a yankunan da ta’addancin ke faruwa.
Ra’ayin masana kan matsalar
Masanin tsaron ya bayyana hakan ne dangane da hare haren da ‘yan bindiga ke zafafa kai wa a yankin arewa maso gabas da kuma arewa maso yamma.
Ya kuma bayyana rashin adalci na kin hukunta masu aikata laifi da aka kama da cewa na cikin dalilan da suka jawo ayyukan ‘yan bindiga ke kokarin dawowa a yankunan da ake gani ta’adin da suke yi a baya sun yi sauki.
“Ga rashin aikin yi ga talauci wanda ke sa matasa shiga kungiyoyin ta’addanci… sannan ga yawan makamai a hannun fararen hula ga kalubalen siyasa da rashin shugabanci nagari duk suna ta’azzara abubuwa”. In ji shi.
Bakoji ya kuma ba da shawara kan hanyoyin da yakamata a bi domin shawo kan matsalar tsaron kasar nan.
Gwamnati ta kara himma wajen inganta tsaro musamman a yankunan da tsaron ya yi rauni. Kungiyoyi na addini da na al’umma su rika shiga tsakani da fahimtar da juna don kawo zaman lafiya ta hanyar wa’azi da wayar da kan al’umma… “ inji Bakoji masani a harkara tsaro.
Mazauna yankin arewa maso gabas da arewa maso yammacin kasar nan da ma wasu sassan kasar na kokawa kan matsalar tsaro, ko da yake hukumomi na ikirarin suna samun nasara kan yan bindiga a yankunan.