
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Harkokin Kasashen Waje A Aikin Hajjin 2025, Sanata Ali Ndume ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dawo da tallafin aikin hajji domin rage wa maniyyata tsadar kudin kujera.
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da BBC, jim kadan bayan kammala aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.
“Akwai bukatar gwamnatin tarayya ta duba yiwuwar dawo da tallafin, wanda gwamnatin da ta gabata ta soke, don saukaka wa al’ummar Najeriya damar gudanar da ibadar.
“A da ana bayar da tallafi wanda ke rage wa jama’a radadi, amma yanzu ba haka lamarin yake ba. Saboda haka, lokaci ya yi da za a dawo da shi,” in ji Ndume.
A shekarar 2025, maniyyata sun biya tsakanin naira miliyan 8.3 zuwa miliyan 8.8, gwargwadon inda suka fito.
Wannan adadi ya karu da kimanin naira miliyan biyu idan aka kwatanta da na bara, lamarin da ya sanya mutane da dama kasa samun damar zuwa aikin hajji.
Sanatan ya kuma bayyana gamsuwarsa da yadda tsarin gudanar da aikin hajji ya kasance a bana, yana mai yabawa hadin gwiwar hukumomin Najeriya da na Saudiyya wajen tabbatar da ingantaccen tsari ga mahajjatan kasar.
A yayin da tattaunawa kan sauya fasalin aikin hajji ke ci gaba a tsakanin masu ruwa da tsaki, wannan kira daga Sanata Ndume na iya janyo sabbin muhawara kan rawar da gwamnati ya kamata ta taka wajen saukaka farashin ibadar ga ‘yan kasa.