Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta kasa (NBA) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji sakamakon cece-kucen da suka taso kan yadda aka samar da su.
Shugaban kungiyar Mazi Afam Osigwe, SAN, ya ce rigingimun da ke tattare da dokokin sun jefa shakku kan gaskiya, sahihanci da amincin tsarin dokoki na kasa.
Ya bayyana haka ne biyo bayan zargin da wani dan Majalisar Wakilai, Honorabul Abdulsammad Dasuki, ya yi na cewa akwai sabani tsakanin dokokin da Majalisar Tarayya ta amince da su da kuma cikakken dokar da aka wallafa ga jama’a.
NBA ta ce, wajibi ne a gudanar da cikakken bincike a fili domin fayyace gaskiyar lamarin tare da dawo da amincewar jama’a ga tsarin majalisa.
Kungiyar ta kuma jaddada cewa ya kamata a dakatar da aiwatar da dokokin har sai an warware dukkan matsalolin da ke tattare da su.
A cewar kungiyar, rashin tabbas a bangaren doka da manufofi na iya illata yanayin kasuwanci, rage amincewar masu zuba jari, tare da barazana ga daidaiton tattalin arziki da bin doka da oda a Nijeriya.
