
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattijai ya bukaci gwamnatin Tarayya da ta binciki zargin tallafa wa Boko Haram da gwamnatin Amurka ta yi a karkashin USAID.
Ndume ya kuma ce, gwamnati bai kamata ta yi watsi da wannan batu ba, la’akari da girman barnar da Boko Haram ta haddasa a jihar Borno da kuma sauran wurare a cikin kasar.
A makon da ya wuce ne, Perry Scott dan Majalisar Datijai na Amurka ya yi Ikirarin cewa, hukumar raya kasa USAID a karkashin gwamnatocin Obama da kuma Biden sun tallafa wa kungiyoyin ta’addanci cikin har da Boko Haram a Najeriya.
Sanatan ya kuma zargi USAID da rashin aiki tare da hukumomin da ya dace a Najeriya. Saboda gwamnatin Trump ta rufe tallafawa ayyukan USAID.
An kafa hukumar USAID a 1960 da ma’aikata 10,000, tare da ofisoshi a sama da kasashe 60, inda take gudanar da ayyukan agaji a fannonin kiwon lafiya, ilimi da kuma rage fatara.
Amman daga baya aka sauya mata alkibla ta bayan fage.