Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da rabon kayan abinci kimanin tirela 100 ga mazauna Ƙaramar Hukumar Ngala waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa na tsawon watanni huɗu.
Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya ya bayyana cewa an raba kayan ne a yankunan Gamboru – Ngala da wasu ƙauyuka da suka fuskanci ambaliyar ruwa.
Kayan abincin da aka raba sun haɗa da Masara da Dawa da Gero inda aka fi bai wa marasa galihu fifiko a rabon.
Gwamnan ya yaba wa shugaba Tinubu da hukumomin gwamnatin tarayya bisa tallafin da suka bayar don tallafa wa waɗanda iftila’in ya shafa.
Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa tana ƙoƙarin rage dogaro da rabon kayan tallafi ta hanyar samar da ayyukan noma don mutanen yankin su riƙa dogaro da kansu.