An danganta rashin kammala aikin titin Abuja zuwa Kano ga ’yan Arewa sakamakon dagewa kan zabin da suka yi na a bai wa kamfani daya.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Yakubu Adam Kofar Mata, a hirarsa a gidan talbijin na Kasa NTA.
Ya ce tuni aka kammala ayyukan titunan kudancin kasar nan tun zamanin mulkin Buhari wanda kuma an fara su ne lokaci daya da aikin titin Abuja zuwa Kano.
Wanda da aka rarraba wa kamfanoni daban daban kamar yadda aka yi a Kudancin kasar nan da tuni an kammala.
Ya kuma ce, yanzu shugaba Tinubu ya basu umarni an kammala aikin cikin kankanin lokaci.
“Don haka mun fara shirye- shiryen gayyato manyan kamfanoni daga kasashen waje domin yin titin kankare aikin hanyar musamman daga Kaduna zuwa Abuja.” Inji shi.
Sannan ya ce, sun fara cike ramuka da farfashewar da hanyar ta yi kafin cigaba da aikin nan bada jimawa ba.
