Za a kara jarin Kamfanonin Rarraba zuwa N500 Biliyan
Majalisar wakilai ta bayar da shawarar ƙayyade Naira biliyan ɗari biyar a matsayin jari mafi ƙankanta na kamfanoni 11 da ke rarraba wutar lantarki na ƙasar nan.
Hakan ya biyo bayan damuwar da ake nuna wa na cewa kamfanonin suna fama da ƙarancin kuɗin aiwatar da ayyukansu, kuma hakan zai sa kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
‘Ƴan majalisar na ganin matuƙar ba a ƙara yawan jarin kamfanonin ba, to ba za su iya ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba na rarraba wutar lantarkin idan an samar .
A maimakon haka ma, sai dai su zama barazana ga ci gaban tattalin arziki Najeriya da kuma jin daɗin jama’a.
Rashin samun wadataccen wutar lantarki a Najeriya ya zama tarnaki ga bunƙasar masana’antu da samar da ayyukan yi da kasuwanci da lafiya da ilimi da sauran bangarori na cigaban rayuwa.
Wanda ake sa ran cewa, Karin jarin na kamfanonin zai magance.