Dalilin da ya sa na kai Ministan Abuja kara kan mabarata – Barista Hikima
Lauyan da ya kai ministan Abuja kara kan kamen mabarata ya bayyana dalilinsa na yin hakan
Barista Abba Hikima dan asalin Kano, mai rajin kare hakkin da Adam ya ce, ya je birnin Abuja ne domin gudanar da wani abu daban amma da ga yadda aikin kwamitin tsaftace garin suke far wa masu bara, sai abin ya sosa masa rai.
Lauyan ya kuma zargi masu kama mabaratan, da kama mutane masu ƙananan sana’o’i da masu ƙaramin ƙarfi da kuma tursasa su.
“Duk da cewa bara ba abin so ba ne, amma ban ji daɗin yadda kamen ya rutsa da mutanen da ba mabarata bane”. Inji shi
A makonnin baya ne, ministan na Abuja Nyesom Wike ya ƙaddamar da matakin kama mabarata waɗanda ya ce sun cika titunan birnin da har sun zama barazana ga tsaro, suna kuma zubar da mutuncin kasar a idon baƙi da ke ziyara.
Yayin ƙaddamar wani aikin titi a Unguwar Katamfe cikin watan Oktoban, Mista Wike ya ce sannu a hankali mabaratan na mayar da birnin Abuja cibiyar mabarata.
A ranar Alhamis ne wata Babbar Kotun Tarayya ta sanya ranar fara sauraron wata ƙara a lauyan yake ƙalubalantar matakin kama mabarata a Abuja.
Yana mai ikirarin cewa hakan saba wa kundin tsarin mulkin kasar ne da y aba kowa damar zama inda yake so.