Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnati za ta duba masu lalurar ido kyauta daga ranar 10 zuwa 15 ga watan da muke ciki.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar zartaswa karo na 20 da aka gudanar a Alhamis din nan.
Ya ce gwamnati ta damu da bangaren lafiya hakan yasa ta bayar da dama ga ma’aikatar kula da harkokin addini da kungiyar matasa musulmi ta duniya domin duba masu ciwon ido kyauta.
Ya ce likitoci za su zo asibitin Sir Sunusi daga sassan duniya domin bayar da magani da yin aiki ga masu lalurar ido.
Haka zalika gwamnan ya yi kira ga iyayen yara da su fito da ‘ya’yansu domin yi musu allurar rigakafin shan inna don kare lafiyar su.