Yau ake sa ran isowar yaran jihar Kano da aka gurfanar a kotun tarayya dake Abuja kan zargin cin amanar kasa yayin zanga-zangar tsadar rayuwa.
A jiya Litinin dai shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin sakin su bayan shan matsin lamba daga yan Najeriya.
Wata sanarwa da daraktan yada labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce gwamna Abba Kabir Yusuf zai tarbi yaran da za a kawo filin jirgin saman Malam Aminu Kano a jirgin Max Air.
Sanarwar ta kara da cewa kafin mika yaran ga iyayensu za a duba lafiyarsu.
Masha Allah