CISLAC ta kalubalanci matakin gwamnonin dake sukar EFCC a Kotun Koli

0
92

Aminu Abdullahi Ibrahim

Ƙungiyoyin ci gaban al’umma da tabbatar da dimukuradiya ciki har da cibiyar dake sanya ido kan ayyukan majalisu ta CISLAC sun yi kira ga kotun koli da ta yi watsi da karar da wasu gwamnonin jihohi suka shigar na kalubalantar dokar da ta kafa hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati da sauran su.

Gamayyar kungiyoyin farar hular karkashin jagorancin babban daraktan CISLAC, Musa Rafsanjani ne suka yi wannan kiran a wata ganawa da manema labarai a Abuja.

Rafsanjani ya ce ya lura cewa karar da ke gaban kotun koli a halin yanzu ba ta shari’a ba ce, kawai zagon kasa ne ga yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Ƙungiyoyin sun kara da cewa matakin gwamnonin barazanace ga yaki da cin hanci da rashawa da kuma ‘yan cin gashin kai na kanannan hukumomi dake zama wani bigire na dimukuradiya tun daga tushe.

Babban Darakta CISLAC ya bayyana matakin da gwamnonin suka dauka a matsayin mafi girman kokarin dakile  tasirin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Ya kara da cewa yinkurin gwamnonin bashi da hurumi cikin doka kuma hakan zai kawo nakasu ga cigaban kasar nan.

Hakazalika Babban Daraktan YIAGA Africa Samson Itodo, ya ce duk kasar da bata gudanar da ayyuka a bayyane, tarbiya da tattalin arzikinta suna kan rugujewa.

Ya ce wajibi ne yan Najeriya su tashi tsaye wajen kare ayyukan EFCC ICPC da sauran Hukumomin da ke da alhakin kare dukiyar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Captcha verification failed!
CAPTCHA user score failed. Please contact us!