Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka Ta Kasa (NCDC) ta ce, an samu karuwar masu dauke da cutar zazzabin Lassa a kasar nan.
A wata sanarwa da Hukumar NCDC ta fitar a shafinta na yanar ranar Talata, ta ce, wasu karin sabbin mutane 10 an tabbatar da sun kamu da cutar a cikin mako na 35 kadai.
An kuma samu mutuwar mutane 162 a jihohi 21 a tsakanin 25 zuwa 31 ga watan Agusta. Sannan an kuma an gano sabbin masu dauke da cutar a jihohin Edo da Ondo da Bauchi da kuma Taraba.
Hukumar ta kuma samu rahoton mutane 7,375 da ake zargi da kamuwa da cutar,a yayin da 871 aka tabbatar sun kamu da cutar a shekarar 2025, tare da adadin masu mutuwa na kashi 18.6 cikin 100, sama da kashi 17.1 cikin 100 da aka samu a daidai wannan lokacin a shekarar da ta wuce.
NNDC ta ce, ta tura tawaga kulawar gaggawa 10 don tallafawa jihohin da abin ya shafa, ta kuma sanar da shirin kaddamar da wani shiri na shekaru biyar daga 2025 zuwa 2029 don magance zazzabin a kasar.
Hukumar NCDC ta ja hankalin ‘yan Najeriya musamman a jihohin da ke fama da matsalar da su kula da tsaftar muhalli, da kuma neman magani da wuri domin rage yaduwar cutar a tsakanin Al’umma
