Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta janye hannunta daga auren da ake shirin daurawa tsakanin jarumin TikTok Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda.
Hisba ta ce wannan ya biyo bayan samun rahotanni da ke cewa akwai sabani da rashin fahimta tsakanin ɓangarorin biyu.
A wani sakon murya da mataimakin babban kwamandan Hisba, Dr. Mujahedeen Aminudden ya fitar, ya ce matasan biyu sun amince za su yi aure domin kwatar kansu daga kotu.
Dr. Mujahedeen yace hukumar Hisbah za ta mayar da mutanan biyu zuwa Kotu domin daukar mataki na gaba.
