Wasu manoma a jihar Zamfara sun koka kan yadda ‘ƴan bindiga ke tilasta musu biyan kuɗin haraji kafin su girbe amfanin gonarsu.
Mazauna ƙananan hukumomin Tsafe da Talatar Mafara sun bayyana cewa ‘ƴan bindigar sun mamaye yankin suna amfani da gonaki a matsayin wurin kai hare-hare, abin da ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin manoma.
Wasu daga cikin manoman da suka yi magana da BBC Hausa sun ce sun biya maƙudan kuɗi kafin ƴan bindigar su amince su shiga gonakinsu don girbi.
Sun kara da cewa, “ƴan bindigar sun tilasta masa sayen lemu, ayaba da ruwan roba na Swan kafin suka bari aka yi girbin gonarsa.”
