
Sanatan Kano ta tsakiya sanata Rufa’i Sani Hanga ya ce, Jami’ar Koyar Da Aikin Gona ta za kafa a garin Kura da Majalisar Dattijai ta amince da kudirin dokar kafata na gab da kammaluwa, da zarar shugaba Tinubu ya sanya hannu a kanta
Hanga ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da manema labarai, ya kuma ce, tun shekarar da ta wuce ya gabatar da kudirin samar da jami’ar, amma sai a wannan shekara ta 2025 majalisa ta amince da kudirin ya zama doka.
Sanata Hanga ya ce, yayi fama kwarai kafin majalisa ta amince da kudirin sakamakon banbancin ra’ayi na wakilan majalisar amma daga bisani ya cimma nasara inda har majalisar ta amince.