Dakarun Rundunar Kare Al’umma da gwamnatin Zamfara (CPG) sun samu nasarar kama wasu mugaggan makamai da ake kyautata zaton an shigo da su ne domin kai wa ‘yan bindiga.
Dakarun tsaron sun gano makaman ne a cikin wata mota yayin da suke gudanar da aikin binciken ababen hawa.
Daga cikin makaman da aka kama akwai bindigogi biyu kirar AK-47, RPG ɗaya, da kuma tarin alburusai.
Wani jami’in rundunar CPG, Salisu Adamu, ya bayyana cewa an kama motar ne a kauyen Dangulbi, inda aka ɓoye makaman a cikin kwalaye da aka cika da kifi domin gujewa zargin wani abu a ciki.
Direban motar, Bashar Mustapha, ya tabbatar da cewa an samu makaman a motarsa.
“Kayan ba nawa bane. Na ɗauko fasinjoji da kayan ne daga tasha ta Gusau zuwa Magami kafin jami’an CPG su tare ni”. In ji shi.
Rahotanni sun ce an mika motar da makaman da aka kama ga hukumomin tsaro domin ci gaba da bincike.
