
Sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, a wata sanarwa da ya fitar, ya yi tambaya kan ko shirin na gyare-gyaren da kuma kudin da ake shirin kashewa ya samu amincewar majalisar dokokin kasar, yana mai bayyana kashe kudaden a matsayin rashin sanin abu mai muhimmanci.
A makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da fara aikin gyara sosai na Legas, wanda aka kiyasta zai ci naira biliyan 712, domin sabunta kayan aikin filin jirgin da ya tsufa da kuma daidaita shi da matakan duniya.
Amma jam’iyyar ADC ta bayyana adadin kudin a matsayin abin al’ajabi da nuna rashin hangen nesa na gwamnatin APC.
ADC ta kara da cewa adadin kudin da za a kashe, daidai yake da kudin da aka kashe wajen gina filayen jirgi hudu a Abuja, Legas, Kano da Fatakwal a 2014 ta hanyar rancen kasar Sin wanda har yanzu ba a gama biya ba.
Jam’iyyar ADC ta kara da cewa da wannan kudin za a iya gina asibitoci guda bakwai, da dauki nauyin ilimin firamare a yankuna uku na tsawon shekaru biyar, da kuma samar da wutar lantarki ga dubban kauyuka, ko gyaran dubban kilomita na manyan hanyoyin kasar nan.
ADC na kira ga ‘yan kasar nan su ki amincewa da wannan shiri maras tushe.