
Jam’iyyar PDP ta soki abin da ta kira yunkurin hana sanata natasha akpoti-uduaghan ta dawo bakin aiki bayan cikar watanni shida na dakatarwar da aka yi mata.
Mai magana da yawun jam’iyyar a ƙasa, debo ologunagba, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a abuja ranar talata.
Sanarwar ta ce wannan yunkuri daga majalisar dattijai na nufin tauye ’yancin wakilcin al’ummar mazabar kogi ta tsakiya a majalisar dattawa.
PDP ta ce hakan ya saɓa da dokokin majalisar da kundin tsarin mulkin ƙasa .
Jam’iyyar ta yi kira ga shugaban majalisar dattawa, godswill akpabio, da ya fito fili ya yi bayani kan batun, tare da tabbatar da cewa ba a yi amfani da ofishin majalisar wajen tauye hakkin sanatar ba.
Jam’iyyar ta kuma shawarci natasha da ta yi watsi da wasiƙar hana ta komawa majalisa, don haka ta shirya komawa bakin aikinta kawai.