
Rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta sake tsara yadda ‘yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) ke gudanar da ayyukansu domin tunkarar matsalolin tsaro na cikin gida.
Babban Sufeton ‘Yan Sandan Olukayode Adeolu Egbetokun ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wata ganawar da ya yi da kwamandodin ‘yan sandan na MOPOL a hedkwatar ‘yan sandan a Abuja.
Wata sanarwa da kakakin rundunar na kasa Olumuyiwa Adejobi ya fitar ya ce, Babban Sufeton ya jaddada buƙatar sake tsara aikin ‘yan sandan domin tunkarar tarzoma da buƙatar gaggawa da kuma barazanar tashin hankali.
“Ya nuna damuwa game da yadda ake juya akalar jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma zuwa ayyukan da ba su shafe su ba, ciki har da rakiya da kuma gadi ga ɗaiɗaikun mutane da kuma manyan mutane, lamarin da ke yi wa ingancin rundunar zagon ƙasa,” in ji sanarwar.
Domin kauce wa wannan matsalar, sufetor janar ɗin ya sanar da wasu matakai ciki har da janye dukkan ‘yan sandan kwantar da tarzoma daga ayyukan da ba a da izinin yi ba da horaswa bayan wata uku-uku kan ɗa’a da aiki bisa ƙa’ida da kuma tabbatar da cewa wasu cikin jami’an na zaune cikin ɗamara suna jiran ko ta kwana a ko wane lokaci, in ji Sanarwar.
Babban Sufeton ‘Yan sandan ya ce, idan jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoman suka aikata ba daidai ba, kwamandojinsu ne za a ɗora wa laifin.
Saboda haka, ya ɓukaci kwamandojin su yi jagoranci na gari da horaswa na lokaci zuwa lokaci da kuma sa ido ta yadda jami’ansu za su yi aiki da ɗa’a da martaba ‘yancin ɗan’adam da kuma inganci.
Najeriya dai tana fuskantar ƙalubale na tsaro a cikin gida, kuma kwanan nan ne wani bidiyo da ya nuna yadda wasu ‘yan China da ke raba wa wasu ‘yan sandan kwantar da tarzomar ƙasar kuɗi ya janyo kakkausar suka a shafukan sada zumunta a ƙasar.