Ma’aikata shida na Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA) da ke Gombe sun rasu, yayin da wasu hudu suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Gombe zuwa Yola.
Hatsarin ya auku ne a yankin Karamar Hukumar Kaltungo ta Jihar Gombe, a lokacin da ma’aikatan ke dawowa daga daurin auren wani abokin aikinsu.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne bayan tayar motar da suke ciki ta fashe a yankin Ladongor, tsakanin Billiri da Kumo a kan hanyar.
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa.
Shugaban Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Gombe, AM Saddam, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutane biyar sun mutu nan take, yayin da maza uku da mace daya ke karbar magani a Asibitin Kwararru na Gombe.
A wata sanarwa da Daraktan Yada Labaran Gidan Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Misilli, ya fitar a daren Litinin, Gwamnan jihar, Inuwa Yahaya, ya mika sakon ta’aziyyarsa bisa rasuwar ‘yan jaridun.
Sanarwar ta bayyana cewa daga cikin wadanda suka rasu akwai Manajar Labarai ta NTA Gombe, Zarah Umar, Manajan Gudanarwar Tashar, Manu Haruna, da Babban Direban tashar, Isah Lawan.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana marigayan a matsayin jajirtattun ma’aikata da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimtawa al’umma ta hanyar aikin jarida, tare da yi musu addu’ar Allah Ya jikansu da rahama.
