Kamal Umar Kurna
Hukumar kwashe shara ta Kano REMASAB, ta fara raba kwandunan shara ga masu baburan adaidaita Sahu a jihar domin kawo karshen zubar da shara barkatai a manyan titunan jihar dan inganta tsaftar muhalli da lafiyar al’umma.
Da yake jawabi a wajen taron rabawar, Shugaban hukumar ta REMASAB, Dr. Muhammad S. Khalil, ya tabbatar da kudurin gwamnatin jihar Kano na tsaftar muhalli da ingantaccen tsarin sarrafa shara.
Dr Khalil ya ce raba kwandunan sharar na daga cikin babbar dabarar da aka tsara domin tabbatar da tarin shara yadda ya kamata, musamman ga masu jigilar jama’a, wadanda suke taka muhimmiyar rawa a zirga-zirgar yau da kullum.
A cewar sa REMASAB za ta yi aiki kafada da kafada da kungiyoyin adaidaita Sahu da Hukumar KAROTA, domin tabbatar da bin dokar, inda yace hukumar sa ta tanadi manyan kwandunan shara a bakin manyan tituna domin bai wa masu Adaidaita Sahu damar zubar da sharar idan kwandon da ke kan baburin su ya cika.
Shima da yake jawabi, Shugaban Kungiyar mamallaka da direbobin adaidaita Sahun, Nazifi B. K. gidan kudi, ya yabawa shirin na REMASAB yana mai cewa hakan zai taimaka matuka wajen tsaftace titunan Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya Mataimakin Shugaban KAROTA, Shu’aibu Lawal Aranposu, ya sanar da bayar da wa’adin makwanni biyu ga masu adaidaita Sahu a Kano domin su mallaki kwandunan shara su fara amfani da su, tare da gargadin cewa hukumar su za ta fara daukar matakin hukunci kan duk wanda ya saba wa umarnin
