
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da Salihu Abdullahi Dembos, tsohon Shugaban Gidan Talbijin na kasa NTA da aka sauke kan mukaminsa.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar a ranar Talata.
Onanuga ya ce, Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a watan Oktoban 2023, ya kuma cire, a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku.
Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙarasa wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027.
A ’yan kwanakin nan ne aka sanar da sauke Dembos sakamakon wasu sauye-sauye da aka gudanar da hukumar.
Sauke shi dai ya janyo zazzafar muharawa da suka musamman daga yankin arewacin ƙasar, inda Salihu Abdullahi Dembos ya fito.