Jamal Umar Kurna
Majalisar dokokin Kano ta fara yin yinkurin yin gyara akan dokar da ta kafa kotu nan shari’ar musulunci, da wadda ta kafa kotuna daukaka kara na addinin musuluncin, domin kaucewa sarkakiyar da ake samu akan hukunce-hukuncen su da na kotu nan Majistare.
Hakan, ya biyo bayan kudurin da mataimakin kakakin majalisar kuma Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Rimin Gado Muhammad Bello Butu-Butu ya gabatar.
Butu-butu yace ko a lokacin da aka kirkiri shari’ar addinin musulunci a Kano, a shekara ta 2000 akwai abubuwa da yawa da ba’a saka a dokar ba, sannan akwai bukatar gyara bangren da zai banbance hurumin da kotu nan musuluncin da na majistare suke da shi akan kowace shari’a.
Butu-butu yace ita kuwa dokar dake tafiyar da kotun daukaka kara na shari’ar addinin musulunci ta zarce shekaru 50 da samar da ita, wanda ya zama dole majalisar tayi mata gyara domin ta dace da zamanin da ake ciki.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewar, majalisar ta kuma ce daga cikin gyaran da zata yiwa dokar, zata bawa bangaren sulhu muhimmanci wanda hakan zai rage yawan cinkoson da ake samu a kotuna da kuma jinkiri wajen shari’a lakari da cewa wasu matsalolin za’a iya magance su ta hanyar yin sulhu.
