
Hamas ta amince ta saki dukkan ƴan Isra’ila da ta ke rike da su.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta amince ta saki dukkan mutanen da take riƙe dasu, masu rai da kuma gawarwakin waɗanda suka mutu, kamar yadda shirin sasanci na shugaba Trump ya gabatar bisa sharadin
Sai dai amincewar na nufin nufin za a shiga ƙarin tattaunawa kan makomawar Zirin Gaza da kuma ƴancin Falasɗinawa.
Sanarwar na zuwa ne sa’oi bayan da shugaba Trump ya ba wa ƙungiyar wa’adin zuwa ranar Lahadi ta amince da tayin yarjejeniyar zaman lafiya ko kuma ta fuskanci mummunar ukuba.
Hamas ta ce, har yanzu ana ci gaba da neman yadda za a cimma matsaya game da makomar Gaza wanda ba a yi batun ba a tayin na Trump.
Shugaba Trump ya fitar da wata sanarwa mai nuna gamsuwa da matsayar da Hamas ta ɗauka amincewa da tayin nasa
“Sakamakon sanarwar da Hamas ta fitar, na gamsuwa cewa sun shirya rungumar zaman lafiya.
“Dole Isra’ila ta daina kai harin bamabamai Gaza domin samun sako mutanen da ake tsare dasu cikin gaggawa.” In ji shi.
An rawaito Ofishin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu na cewar “Biyo bayan sanarwar Hamas, Isra’ila za ta aiwatar da zangon farko na yarjejeniyar zaman lafiya ta Trump domin gaggauta sakin mutanen da Hamas ke tsare da su’.