Shugaba Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron ƙasar Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata
Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Tinubu ya aika wasiƙa ga shugaban majalisar dattawan ƙasar Godswill Akpabio inda yake sanar da shi naɗin.
Janar Musa mai ritaya ya maye gurbin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga muƙaminsa ranar Litinin.
