
Amurka ta sanar da rage wa’adin biza da kuma dalilan bayar da bizar ga yawancin ‘yan Najeriya masu shiga kasar
A sanarwar da Ma’aikata da harkokin kasashen waje ta fitar ta ce matakin ya fara aiki ne tun daga ranar 8 ga watan Yuli.
Ma’aikatar ta ce, daga yanzu dukkanin bizar da za ba wa ‘yan Najeriya ta masu zuwan wucin-gadi ce, ba kuma ta diflomasiya ba. Bizar za ta kasance ne ta shiga daya mai wa’adin wata uku ne sabanin da yadda take bayar da biza daya da wa’adin shekara daya ko ma fin haka kuma.
A sanarwar ta kuma ce tana aiki hannu da hannu da hukumomin Najeriya domin tabbatar da ganin kasar ta daidaita al’amuranta musamman bayar da takardun tafiye-tafiye masu tsaro da hana wuce wa’adin zama a kasar da kuma musayar da bayanan da suka shafi tsaro ko wani mugun laifi a ssaboda dalilai na kare lafiyar jama’a.
‘Yan Najeriya masu yawon buɗe idanu da dalibai da ‘yan kasuwa masu tafiye tafiye na daga cikin waɗanda wannan sauyi mai tsauri na bayar da bizar Amurkar zai shafa.