
Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun kai hari kan mashigar hedkwatar rundunar sojin Syria da ke tsakiyar birnin Damascus babban birnin kasar.
Tashar talabijin ta Isra’ila ta ruwaito cewa a kalla mutane biyu sun jikkata a harin, duk da cewa ba a fadi cikakken wajen da lamarin ya faru ba.
Haka kuma, rahotanni sun ce an jiyo karar harbe-harbe a kusa da ginin hedkwatar rundunar sojin Syria.
Gidan rediyon kasar Isra’ila ya tabbatar da kai harin, inda ya bayyana cewa an nufi kayayyakin sojin Syria da ke yankin.
Isra’ila ta kara da sanar da shirin tura karin dakarunta zuwa yankin iyakarta da Syria, domin kare lafiyar kasa, a cewarta.
Wannan hari na zuwa ne bayan wata sabuwar barazana daga Ministan Tsaron Isra’ Yoav Gallant, wanda ya ce za su ci gaba da kai farmaki kan dakarun Syria, musamman idan ba su janye daga yankin Sweida ba, inda ake fama da rikici tsakanin al’ummar Druze da Bedouin.