
Wata kungiya mai bin diddigin ayyukan kasafin kudi (Budgt) ta zargi ‘yan majalisar dokoki na kasa da cushen wasu ayyuka marasa amfani cikin kasafin kuɗi.
Rahoton kungiyar ya bayyana cewa an saka kwangiloli har 11,122 a kasafin kuɗi na shekarar 2025, waɗanda za su lashe kuɗi har naira tiriliyan 6.93, ba tare da cancanta ko amfani kai tsaye ga jama’a ba.
Wasu daga cikin waɗannan ayyuka sun haɗa da rabon takin zamani da bayar da tallafin karatu da gina cibiyar koyar da kwamfuta (ICT/CBT) da kuma sayen motoci na tsaro, duk da cewa ba su da alaƙa da aikin ma’aikatar da aka sanya su a cikinta.
BudgIT ta ce, waɗannan ayyuka da aka cusa a kasafin kuɗi sun kai kashi 12.5 cikin 100 na duk kuɗaɗen kasafin kuɗin Naira tiriliyan 54.99 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da su.
Ƙungiyar ta kuma ce, wannan ɗabi’a tana rage tasirin kuɗin gwamnati, tana kuma sa jama’a rasa amana da gwamnati.
BudgIT ta buƙaci gwamnati da ta riƙa kwatanta gaskiya da adalci wajen tsara kasafin kuɗi, domin a tabbatar kuɗin na yi wa jama’a amfani kai tsaye.