
Sakataren Gwamnati da wasu Malamai 'yan kwamitin
Manyan malamai na jihar Kano sun fara zaman Majalisar Shura domin sauraron korafe-korafen da aka mika musu kan zargin batanci da ake yiwa Malam Lawal limamin Masallacin Triumph.

Sakataren Gwamnatin Jihar ne, ya tura ƙorafe-ƙorafen a ranar Juma’a, inda kwamitin ya fara zama domin sauraronsu.
Sakataren kwamitin, Shehu Wada Sagagi, ya shaida wa manema labarai za su tabbatar da adalci.

“Bayan mun saurari ɓangarorin biyu, kwamitin zai tattauna sannan ya bai wa gwamnatin jiha shawarwari,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin masu ƙorafin sun yi barazanar kai ƙara kotu, amma ya roƙe su da su bari kwamitin Shura ya yi aikinsa.

Wannan mataki ya zo ne biyo bayan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na mika batun ga majalisar, domin ta yi cikakken nazari tare da bayar da shawarwari kan yadda za a magance lamarin cikin adalci, gaskiya da kuma mutunta doka da tsarin addini.
Majalisar ta jaddada cewa za ta yi aiki bisa gaskiya, da kuma yin la’akari da kare mutuncin Annabi (SAW), da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jihar Kano da ma kasa baki da