Rundunar ‘yansandan Jihar Neja ta kama mutane 11 bisa zargin shiga harkar ƙungiyoyin asiri da kuma satar kifin wani mutum.
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun ya ce an kama Idris Hamza da Suleiman Damilare a unguwar Fadikpe da tabar wiwi da kayan tsafi da mota ƙirar Toyota a gidan wani Abdullahi Ahmed da ake kira Catch-up.
Wadanda ake zargin sun amsa cewa su ‘yan ƙungiyar asiri ne sun kuma bayyana cewa suna gudanar da ayyukansu a jihar har da ɗaukar sabbin mambobi a Jami’ar IBB dake Lapai.
Binciken ya kai ga kama wani Abdulsemiu Basir, wanda ake zargin shima ɗan ƙungiyar asirin ne.
An kama shi a tashar mota a Lapai tare da abubuwan da suka hada da layin waya guda 16, na’urar POS, da kuɗi har Naira 77,000.
