
Tsohon Ministan Shari’a na kasa, Abubakar Malami, SAN, ya yi watsi da iƙirarin da wasu ƴan tsohuwar jam’iyyar CPC da ta narke cikin haɗakar APC -suka yi na nesanta tsohuwar jam’iyyar daga ficewa daga haɗakar.
A farkon makon nan ne wani tsagin tsohuwar jam’iyyar CPC ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Nasarawa, Umaru Tanko Almakura suka yi taro a Abuja, inda suka jaddada goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Tinubu tare da nesanta kansu daga ficewa daga APC.
Daga cikin waɗanda suka harci taron har da tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da tsohon ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu da Hon Farouk Adamu Aliyu, tsohon ɗan majalisar daga jihar Jigawa da wasu ƙusushin tsohuwar CPCn.
To sai toshon Ministan ya yi watsi da wannan iƙirari da tsagin Almakuran suka yi, yana mai bayyana matsayar tasu da ta raɗin kai ba da yawun tsohuwar tafiyar CPCn ba.
Cikin wata sanarwa da kakakin tsohon ministan, Muhammad Bello Doka ya fitar, ya ce jagorancin tsohuwar jam’iyyar CPCn ne kawai ke da alhakin fitar da matsayar tsohuwar jam’iyyar kan kan batun fita daga APC, ba tsagin su Almakura ba.
Malami ya zargi Tanko Al-Makura da Adamu Adamu da Aminu Bello Masari da kuma Farouk Adamu Aliyu ya janye jikinsu daga jikin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.
Dangane da batun komawarsa jam’iyyar SDP kuwa, Malami ya ce aikin masu yaɗa jita-jita ne, amma ya ce yana kan tattaunawa da magoya bayansa kan batun.