Shugabar riƙo ta Venezuela, Delcy Rodriguez, ta yi kiran sakin shugaban ƙasar Nicolas Maduro tare da mai dakinsa tare da shan alwashin ”kare” ƙasar.
Shugaba Trump dai ya ce Miss Rodriguez na son aiki da Amurka, yayin da ya ce jagorar adawar ƙasar, Maria Corina, da aka zaci ita ce za ta dare karagar mulkin kasar, ba ta samu cikakken goyon bayan da ake bukata ba.
Tun da farko shugaba Trump ya ce ƙasarsa ce za ta ja ragamar ƙasar har zuwa lokacin kafa sabuwar gwamnati.
Jagoran ɗariƙar Katolikan na duniya Fafaroma Leo ya ce dole ne a tabbatar da martabar Venezuela tare da walwalar ƴan ƙasar fiye da komai.
Itama kasar China ta yi kiran a gaggauta sakin Shugaba Maduro, tana mai cewa Amurka ta keta dokokin duniya.
Ana sa ran Mista Maduro zai gurfana a gaban kotu ranar Litinin domin fuskantar tuhume-tuhume kan safarar miyagun ƙwayoyi da makamai, zarge-zargen da a baya ya sha musantawa.
A gobe ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taro domin tattaunawa kan harin da Amurka ta kai wa Venezuela tare da kama shugaban ƙasar da mai ɗakinsa.
